Shugaban Kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya fadi cewa Wajibi ne ga dukkan gwamnatin kasashen yanki su tunbuke tushen ta’adanci baki daya
Shguaban Rohani ya fadi hakan ne a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Kazakistan a wata ziyara da ya kawo nan birin Tehran a yau Asabar , yace bisa la’akari da kwarewar da kasar Iran take da shi wajen kere-kare kamar kera layin dogo da wutar lantarki da kayakain Asibiti , don haka kofa a bude take ga gwamnatin kasar kazakistan da ma sauran kasashen yanki wajen kula kyakykawar dangantaka tsakaninsu da Iran yadda za ci gajiyar juna
A nashi bangaren shugaban kasar Kazakistan Alamas Big Atambayef ya jaddada game da muhimancin sanya kasar Iran a cikin jerin kungiyar kasashen Shangai, daga karshe ya yi ishara game da kungiyoyin yan ta’adda da suke samun goyon baya da taimakon kudi da makamai daga kasashen Turai, domin bakanta fuskar musulunci a idon duniya, don haka kasarsa a shirye take ta yi aiki da dukkan kasashen yanki domin yaki da ta’adanci da tsattsauran ra’ayin Addinin.